1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WFP: Gaza na cikin halin yunwa

May 5, 2024

Daractar Hukumar Abinci ta Duniya, Cindy McCain ta yi gargadin kan matsanancin yunwa da ake fuskanta a Gaza.

https://p.dw.com/p/4fW4j
Hukumar Abinci ta Duniya ta ce ana fama da matsanancin yunwa a Gaza
Hukumar Abinci ta Duniya ta ce ana fama da matsanancin yunwa a GazaHoto: Habboub Ramez/abaca/picture alliance

Cindy McCain ta yi wannan gargadi ne a lokacin da ake zantawa da ita a kafar yada labarai a Amirka. Daractar ta yi fatan a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan kusa domin su samu damar ci gaba da shigar da agajin abinci da ruwa da magunguna zuwa yankin.

Karin bayani:Majalisar Dinkin Duniya ta ce yunwa na kisa a Gaza 

A cewarta akwai isasshen abincin da za a iya taimakawa wadanda yaki tsakanin Isra'ila da Hamas ya rutsa da su. A watan Maris din da ya gabata ne dai, masana suka yi gargadin cewa al'ummar Gaza za ta fada cikin iftila'in yunwa a watan Mayu.